Wata Kotu a Kano ta aike da wasu matasa 4 yan TikTok gidan gyaran hali biyo bayan karar da Hukumar tace Fina-finai ta shigar gabanta
Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano Alh. Abba ya jaddada aniyarsa ta kawo karshen aiyukan rashin da'a da ke yawaita a kafafen sada zumunta na zamani a Jahar Kano inda a yau Hukumar ta samun nasarar kama wasu matasa guda 4 masu amfani da manhajar TikTok da ake zargi da nuna rashin tarbiya tare da kalamai marasa ma'ana inda la'akari da hakan laifi ne a dokar Hukumar ta yanke shawarar kaisu gaban kotu domin girbar abinda suka shuka.
Tunda farko da farko bayan mai gabatar da Kara Brr. Garzali Maigari Bichi ya karantowa wanda ake zargi tuhume-tuhumensu wato Hafsa Hamisu (Zoom Zoom), Usman Majidadi (Majidadi) Sumayya Muhammad (Summy Beby) da Usman Ibrahim (Maikalar Kudi), inda dukkanninsu nan take suka amsa saide mai shari'ar dake kotun no-man's-land Hajiya Halima wali ta dage sauraran karar daga 28/5/2025 zuwa 2/6/2025 tare da bada umarnin a ajiyesu a gidan gyaran hali har ranar da za'a dawo domin yanke hukunci.
Idan ba'a mantaba a watanin da suka gabata Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano ta aike da irin wannan matasa gaban kotu domin ladaftar dasu inda kotun bayan samunsu da laifi kotun ta yanke musu hukuncin daurin shekara daya ko zabin biyan tara na kudi nera dubu Dari daya (100,000) tare da wanda zasu karbesu da sharadin irin haka bazai kara faruwa dasu ba.
Wannan de wani yunkuri ne da Hukumar tace fina-finai ta Jahar Kano ke yi tsawon lokaci domin kawo gyara tare da dakile irin rashin tarbiyar da wasu matasa ke nunawa a kafafen sada zumunta a Jahar Kano wanda yin hakan yaci karo da tsarin al'ada tare da koyarwar addinin musulunci.