Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa (yankin kudu maso gabas), Ijeoma Arodiogbu, ya bayyana cewa gwamnonin jihohin Bayelsa, Rivers, Plateau da Kano za su sauya sheka zuwa jam’iyyar mai mulki cikin watanni biyu masu zuwa.
A wata hira da jaridar Punch, Arodiogbu ya ce shirin sauya shekar ba zato ba ne ko jita-jita, illa dai wani abu da zai faru nan ba da jimawa ba.
Ya kara da cewa jam’iyyar APC ba ta rufe kofa ga yiwuwar Gwamna Peter Mbah na Enugu da takwaransa Alex Otti na Abia su ma su koma APC ba.
“Ina magana ne akan gwamnonin Bayelsa, Rivers, Plateau, Kano, ko dai Abia ko Enugu. Cikin watanni biyu masu zuwa, za ku ga sun shiga jam’iyyarmu a hukumance,” in ji shi.
“A bayyane yake cewa Bayelsa na cikin lissafin nan — shi yasa na ambace ta. Game da Adeleke (Gwamnan Osun), ba zan iya bayar da tabbaci ba, amma na san yana ta yin wasu yunkuri.”
Arodiogbu ya ce ‘yan siyasar adawa da ke kokarin hada kawancen jam’iyyun adawa domin fuskantar zaben 2027, burinsu kawai shi ne su fito a kafafen yada labarai, ba don mulki ko ci gaban kasa ba.