Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana cewa nasarar Najeriya kan ‘yan ta’adda da dukkan makiyan kasa tabbas ce.
Janar Oluyede ya sake jaddada kudirin rundunar sojin Najeriya na kawar da ta’addanci tare da tabbatar da tsaron kasa ta hanyar dabarun yaki da ta’addanci masu inganci.
Ya fadi hakan ne a yayin bikin addu’ar cocin addinai daban-daban da aka gudanar domin bikin ranar rundunar sojin kasa ta Najeriya na shekarar 2025 a ranar Lahadi a birnin Abuja.
Ya kara da cewa sojin Najeriya ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kare ikon kasa da kuma kare ‘yancin dukkan ‘yan Najeriya.
“Ba za mu taba barin darajar mu ba, wacce ke da nasaba da bangaskiyarmu, kuma za mu ci gaba da rayuwa bisa taken rundunar sojin Najeriya wato: ‘Nasara daga Allah kadai take.’”