Shugaba Tinubu ya nada Dan Kano Isma'il Ahmed a matsayin Shugaban shirin Gwamnati na samar da Gas na PCNG
Wannan na cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Jumu’a 27 ga Yuni 2025.
Sanarwar ta ce Ismaeel Ahmed zai jagoranci shirin PCNGi wanda aka kirkiro domin rage raÉ—aÉ—in cire tallafin man fetur, ta hanyar samar da makamashi mai rahusa da tsafta wato iskar gas da aka matse (CNG).
Tuni dai shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya naÉ—a Barrister Ismaeel Ahmed a matsayin Shugaban Shirin, a yunkurin da zai yi wajen kawowa shirin na gwamnati ci gaba.