WHO ta koka kan yadda kwararru suka kasa gano dalilin barkewar cutar Corona
Hukumar lafiya ta duniya ta ce har yanzu ta gaza cimma burinta na gano ta inda cutar Corona ta faro da kuma dalilin fantsamarta zuwa sassan duniya, kuma har yanzu babu cikakken bayani kan abinda ke hana binciken nata cimma nasara.
Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana hakan, yana mai cewa hukumar za ta yi duk mai yiwuwa don bankaɗo gaskiyar lamarin, yana mai cewa ko a baya-bayan nan sai da aikin binciken na wasu gungun ƙwararru ya kasa cimma nasara.
Cutar Corona na cikin cutukan da suka fi gigitar da duniya, wadda ba za’a taÉ“a mantawa da ita a duniya ba, la’akari da yadda ta yi sanadin mutuwar miliyoyin mutane, da kuma tilasta sanya dokar hana shige da fice matakin da ya tsayar da duniya cak.