Abba Gida-Gida Ya Biya Naira Biliyan 22 Daga Cikin Biliyan 48 Da Ya Gada Na 'Yan Fansho
A wani yunkuri na dawo da mutunci ga tsoffin ma’aikata da iyalan ma’aikatan da suka rasu, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya biya Naira biliyan 22 daga cikin naira biliyan 48 da gwamnatin da ta gabata ta bari na bashin fansho.
Wannan mataki na Gwamna Yusuf ya biyo bayan amincewarsa da fitar da kaso na hudu na biyan kudaden, wanda ya kai naira biliyan 6, lamarin da ya kawo sauÆ™i da farin ciki ga daruruwan tsoffin ma’aikata da iyalan wadanda suka rasu da suka dade suna jiran hakkokinsu.
Tun da farko, Gwamnan ya fitar da naira biliyan 5 a matakin farko, sai naira biliyan 6 a mataki na biyu da kuma biliyan 6 a mataki na uku, wanda ke nuna jajircewarsa na biyan wannan bashi da gwamnatin baya ta bari.
A wata sanarwa da Kakakin Gwamnatin Jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, ya bayyana cewa wannan biyan fansho da kudaden wadanda suka rasu, na daga cikin shirin Gwamnan na magance matsalolin da suka dade suna ciwa al’umma rai tare da mayar da jihar Kano abar koyi ta fuskar nagartaccen shugabanci.
“Gwamna Yusuf ya tsaya tsayin daka akan alkawarin da ya dauka na biyan duk wata naira da tsoffin ma’aikata da iyalan ma’aikatan da suka rasu suke bi bashi,” inji sanarwar.
Biyan wadannan kudade ba kawai ya rage wahala da rashin kwanciyar hankali da waÉ—anda abin ya shafa ke ciki ba, har ma ya Æ™ara tabbatar da cewa wannan gwamnati ta kuduri aniyar dawo da amincewar jama’a da tabbatar da adalci a cikin al’umma.
Gwamna Yusuf ya kuma sake jaddada cewa saura ragowar bashin za a ci gaba da biyansa a wasu kaso na gaba, domin tabbatar da cewa babu wani mai hakki da za a bari.
Wannan mataki na tarihi yana bayyana salon shugabanci mai nuna damuwa da jin Æ™ai ga jama’a, wanda ya kawo fata da kwarin gwiwa ga dubban mutane da suka sadaukar da rayuwarsu wajen gina Jihar Kano.