Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce ba ya ganin matatun man gwamnati da ke Port Harcourt, Warri da Kaduna za su iya dawowa aiki yadda ya kamata duk da kashe sama da dala biliyan 18 da NNPC wajen gyara su.
Dangote ya bayyana haka ne a matatarshi lokacin da ya karɓi baƙi daga makarantar harkokin kasuwanci davke Lagos.
Ya ce gyaran matatun gwamnati tamkar gyara motar da aka kera shekaru 40 da suka wuce ne, duk da cigaban fasaha da aka samu.
Ya ce matatarshi na tace fiye da kashi 50% na man fetur, yayin da matatun gwamnati ke iya tace kashi 22% kawai.