Hukumar Shari'a hadin gwiwa da Hukumar tace fina finai da Dab'i ta jihar Kano sun kulla alakar aiki domin tsabtace tare da gyaran tarbiyya a jihar.
Wannan na zuwa ne a wata ziyara da hukumar ta Shari'a karkashin Jagorancin Kwamishina na 2 Sheikh Ali Danabba.
Sheikh Danabba yace sun kai ziyarar ne domin karfafa musu gwiwa hadi da bada shawarwarin da suka dace tare kuma da hada hannu wajen tabbatar da ingantacciyar tarbiyya a jihar ta Kano Baki Daya.
"Muna yaba maka bisa ga yadda muke tunani akan ka ba haka muka gani ba, domin aikin da kakeyi abin a yaba maka ne" Cewar Sheikh Danabba
A jawabinsa Shugaban Hukumar tace fina-finai Alhaji Abba El-mustapha ya bayyana wannan ziyara a matsayin wani kaimi da akaiwa hukumar ta tace fina-finai tare da Alkawarin hada hannu domin tafiyar da ita yadda ya kamata bisa tsari na tarbiyyar musulunci.
"Shi aiki idan akwai wanda zasu taimaka maka, yafi tafiya yadda ya kamata, zamuyi duk kokarin mu domin ganin mun hada hannu da ku, domin a tsabtace aikin mu" cewar El-mustapha
A karshe Sheikh Ali Danabba ya kuma yabawa Abba El-mustapha bisa ga yadda yake kokari domin ganin an dakatar da dukkanin wasu fina finai da ake ganin zasu lalata tarbiyyar Al'umma.