Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, ya tsaya a matsayin mai tsaya wa wani da ake zargi da manyan laifukan safarar miyagun kwayoyi, Suleiman Danwawu, bayan kotu ta gindaya masa sharudan beli masu tsauri.
Kotun Tarayya a Kano, karkashin mai shari’a MS Shu’aibu, ta amince da belin ne bayan ta bukaci a kawo kwamishina mai aiki a gwamnatin Kano a matsayin mai tsaya masa, tare da sanya shi ya ajiye kudi Naira Miliyan Biyar a asusun ajiya.
Wata majiya ta rawaito cewar a ranar 18 ga Yuli, kwamishinan sufuri, Namadi, ya rubuta takarda zuwa kotu yana rokon a amince ya tsaya wa Danwawu, tare da sha alwashin cewa zai tabbatar da ya kawo shi a duk lokacin da aka dage shari’ar.
Hukumar NDLEA ce ta gurfanar da Danwawu kan tuhumar laifuka takwas na safarar miyagun kwayoyi, kuma NBA reshen Kano ta bayyana cewa za ta sa ido sosai a kan shari’ar.
Manema labarai sun tuntubi Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, domin ya yi tsokaci kan lamarin, amma ya ce yana cikin taro ne a lokacin kuma zai kira daga baya.
Sai dai har zuwa lokacin da ake kammala rubuta wannan rahoton, bai sake kiran ba kuma bai yi wani karin bayani ba.