Zamfara: Sarkin Gusau, Ibrahim Bello ya rasu yana da shekaru 71
Sarkin Gusau, Dakta Ibrahim Bello, ya rasu a jiya Alhamis a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya.
Sakataren Majalisar Masarautar ne Alhaji Sambo A. Sambo ne ya bayyana hakan, inda ya ce sarkin ya rasu yana da shekaru 71 a duniya.
An nada Dr. Ibrahim Bello a matsayin sarki a ranar 16 ga Maris, 2015, a zamanin tsohon Gwamna, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar.
Marigayin shi ne Sarkin Gusau na 15, kuma jinin Shehu Usman ÆŠan Fodiyo ne.
Marigayin ya bar mata da 'ya'ya da jikoki da dama. Ya kasance Æ™wararren ma’aikacin jinya (nurse) wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunÆ™asa fannin kiwon lafiya a jihohin Sokoto da Zamfara.