Sojojin Operation Hadin Kai sun dakile harin da Boko Haram suka yi shirin kaiwa a Monguno da Bitta a Jihar Borno, inda su ka kashe 'yan ta'adda da dama, ciki har da wani kwamandan Boko Haram.
A cewar sanarwa daga Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Rundunar Sojojin Kasa, Kyaftin Reuben Kovangiya, sojojin sun dakile harin da ƴan ta'addan suka yi ƙoƙarin kaiwa Monguno da jarumtaka.
“Dakarun da suka nuna jajircewa yayin Æ™oÆ™arin shiga cikin garin da 'yan ta'addan suka yi, sun gwabza da su da karfi da karfe, lamarin da ya kai ga kashe 'yan ta'adda da dama, ciki har da wani babban kwamanda mai suna Ibn Khalid, da kuma mai daukar bidiyon su,” in ji shi.