Jam’iyyar APC ta zaɓi sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.
Shugaban Gwamnonin APC kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ne ya gabatar da kudirin na nada Ministan Jin Kai a matsayin Shugaban Jam’iyyar, inda Kakakin Majalisar Wakilai, Abba Tajudeen, ya mara masa baya.
An zabe shi ne a taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na APC da ke gudana a Abuja a yau Alhamis.
Yilwatda ya gaji Abdullahi Umar Ganduje, Wanda ya yi murabus a watan da ya gabata.