Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana dalilin ganawar sirri da ya yi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa a Abuja.
Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, ya tabbatar da ganawar ga manema labarai, inda ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan harkokin siyasa da kuma yadda ake tafiyar da mulki a halin yanzu.
“Mun tattauna ne kan batutuwan da suka shafi siyasa da kuma gudanarwar gwamnati. Zan ci gaba da yin aiki da shugaban kasa Bola Tinubu,” in ji Kwankwaso, sai dai bai bayyana cikakkun bayanai game da yarjejeniyar da suka cimma ba.
An gudanar da ganawar ce bayan kammala taron masu ruwa da tsaki kan tattalin arzikin kasa da aka yi a dakin taro na fadar shugaban kasa a ranar Litinin.
Wannan ita ce ganawa ta biyu tsakanin Kwankwaso da Shugaba Tinubu cikin shekara guda da rabi, tun bayan haduwarsu ta farko a watan Yunin 2023, kwana kadan bayan rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasa.