A ranar Litinin ne tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya yi wata ganawar sirri da shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa.
Taron ya biyo bayan bayyanar Kwankwaso ne a wajen bude taron tattalin arzikin gandun daji a Najeriya na shekarar 2025 da aka gudanar a babban dakin taro na fadar gwamnati, Abuja.
Wannan dai shi ne ce karo na biyu da aka hadu a bainar jama'a tsakanin mutanen biyu cikin sama da shekaru biyu.
Ganawar da suka yi na karshe a fadar Aso Rock Villa ta faru ne a ranar 9 ga watan Yuni, 2023, kwanaki bayan rantsar da Tinubu, wanda hakan ya sa Kwankwaso ya zama dan takarar shugaban kasa na farko da ya ziyarci shugaban kasa.
Da yake jawabi ga manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan tattaunawar, Kwankwaso ya ce ya tattauna da shugaban kasa kan harkokin siyasa da mulki.
Ya kuma ce yana iya yin aiki da Tinubu, amma bai bayyana cikakken bayani ba.
Duk da cewa taron na ranar Litinin ba a bude wa manema labarai ba, ziyarar ta zo ne makonni kadan bayan da jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress ta sanar da kafa kawancen hadin gwiwa da nufin kalubalantar jam’iyyar All Progressives Congress a zaben 2027.
Mai bayani: Kwalara
Da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar a lokacin, Kwankwaso ya ce ya tattauna da shugaban kasa kan harkokin siyasa da mulki.
Ya kuma ce yana iya yin aiki da Tinubu, amma bai bayyana cikakken bayani ba.
Ziyarar ta zo ne makonni kadan bayan da jam’iyyar adawa ta ADC ta sanar da kafa kawancen hadin gwiwa da nufin kalubalantar jam’iyyar APCa zaben 2027.
Kwankwaso, mai shekaru 67, gogagge ne a Arewa kuma ya kafa kungiyar siyasar “Kwankwasiyya”.
Ya yi wa’adi biyu a matsayin gwamnan Kano (1999-2003 da 2011-2015), ya zama ministan tsaro a karkashin shugaba Olusegun Obasanjo kuma ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP a 2023, inda ya zo na hudu amma ya samu gagarumar nasara a jihar Kano.
Jam’iyyar NNPP ta lashe kujerar gwamna da mafi yawan kujerun ‘yan majalisar jiha, lamarin da ya tabbatar da ci gaba da tasirin Kwankwaso a jihar da ta fi kowacce yawan al’umma a Najeriya.
Duk da cewa jam’iyyar NNPP ba ta cikin jam’iyyar ADC a hukumance, ‘yan adawa sun yi zawarcin Kwankwaso a yayin da suke neman hada kan ‘yan jam’iyyun hamayya kafin zaben shugaban kasa na 2027.
Majiyoyin fadar shugaban kasa da aka tuntuba game wannan ganawa ba su iya tabbatar da cikakken bayanin tattaunawar da mutanen biyu suka yi ba.
Wata majiya ta ce an gudanar da taron ne a gidan Shugaban ƙasa ba a ofis ba, don haka, an haramta wa galibin hadimai shiga wurin tattaunawar.