Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci a dauki matakai masu tsauri kan masu aikata cin zarafin mata a Jihar Kano, yana mai cewa babu musulmi nagari da ke dukan matarsa.
Ya koka kan yadda laifukan fyade da na dukan mata daga mazajensu ke kara yawaita a jihar, yana mai cewa malamai da limamai na da rawar da za su taka wajen sauya dabi’un al’umma domin kawo karshen wannan barna.
Daily Trust ta rawaito cewa Sanusi ya yi wannan kiran ne a yau Litinin yayin da ya karɓi awagar cibiyar bincike da aiwatar da aiyukan ci bgaba (dRPC) da kuma Cibiyar Musulunci da Tattaunawar Addinai ta Jami’ar Bayero (CICID) a fadarsa da ke Kano.
A cewar Sarkin: “Ni ban yarda da dukan mace ba kuma wadanda suke yi ba don gyara suke yi ba. Abin da muke gani yanzu shi ne duka mai tsanani da jikkata mata da sunan gyara.
"Addinin Musulunci ya girmama mata fiye da kowanne addini, kuma duk wanda ke fakewa da addini domin cin zarafi ko dukan mace, bai fahimci addinin ba.
"Duk wanda ke dukan matarsa har ya jikkata ta, ba mutum nagari ba ne. Ni ban fada ba, Annabi Muhammadu (SAW) ne ya fada. Masu karatu ne kadai za su fahimta," in ji Sarkin.