Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II phD CON, ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar korafin al'ummar Unguwar Daneji dake zaune a kusa da Gidan Ahmad Idris a unguwar daneji dake karamar hukumar Birni a jihar Kano.
Sarkin ya kuma gargadi tsohon akanta janar Ahmed Idris daya sani duk abin daya samu al'ummar yankin shine silar faruwar hakan, sannan ya bukaci hukumomi da Jami’an tsaro su gaggauta daukar matakin daya dace don tseratar da rayuwar al’umma daga barazana.
Mai martaba Sarkin ya bukaci Jami’an tsaro da Gwamnatin jihar dasu gaggauta daukar matakin gaggawa don tseratar da Rayuwar al'ummar yankin, wanda daga bisani Sarkin ya bukaci Mazauna Unguwar ta Daneji dasu sa ido akan dukkan wasu abubuwa da ka iya zama barazana ga lafiyarsu.