Jami’an hukumar hana fasa kwauri ta Æ™asa Costom sun kama kuÉ—aÉ—e Naira miliyan 653 da ba wanda ya yi ikirarin nasa ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
Hukumar ta sanar da haka ne lokacin da ta ke miƙa kuɗin da mutane uku da ake zargi ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC domin ci gaba da bincike.
Shugaban ofishin Costom na Yankin Kano da Jigawa, Dalhatu Abubakar, ya ce an kama kudaden ne bayan samun bayanan sirri da kuma bincike da jami’ansu suka gudanar a filin jirgin.
Ya ce an dakatar da wani fasinja mai suna Ahmed Salisu, wanda ke dauke da fasfo na Ghana, bayan ya iso daga Saudiyya cikin jirgin Ethiopian Airlines.
Shugaban ya ce binciken kayayyakin da fasinjan ke dauke da su ya kai ga gano kudaden kasashen waje da aka boye a cikin katon-katon na kaya.
Kudaden da aka gano sun hada da dala $420,900, fam £5,825, CFA miliyan 3.9 da CFA 224,000 wadanda aka kiyasta darajarsu zuwa N653.9 miliyan.
Abubakar ya ce wanda ake zargin bai bayyana wadannan kudade a lokacin isowarsa ba, kamar yadda doka ta tanada.