Kotun Tarayya Ta Kano Ta Karɓi Karar Da Aka Shigar Da FRSC Kan Tsayawa Da Binciken Motoci A Titunan Jihohi
Lauya Abba Hikima, Esq. ya shigar da kara a gaban babbar Kotun Tarayya da ke Kano, yana kalubalantar hukumar Federal Road Safety Commission (FRSC) da kuma kwamandan hukumar a Kano, Mohammed Bara’u Bature, kan abin da ya bayyana a matsayin take hakkin 'yan kasa da cin zarafi ta hanyar tsayawa, bincike da tsare motoci a titunan da ba na tarayya ba.
An shigar da karar a matsayin shari’ar kare hakkin bil’adama da maslahar jama’a (Public Interest Litigation), inda lauyan ke neman kotu ta fassara cewa hukumar FRSC ba ta da hurumin aiki a titunan jiha da na kananan hukumomi.
Lauya Abba Hikima ya bukaci kotu ta yanke hukunci akan abubuwa kamar haka:
1. Bayani (Declaration) cewa duba da dokar da ta kwace ikon FRSC daga aiki a kan titunan jiha da na kananan hukumomi, to abin da jami'an FRSC suka yi masa na tsayawa, tambaya, da bukatar lasisin mota a Kano ranar 1 da 2 ga Yuli, 2025, yana ci gaba da tauye masa ‘yancin Dan-Adam da yanci na zirga-zirga da ke karkashin sashe na 35 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
2. Bayani (Declaration) cewa babu wata doka ko kundin tsarin mulki da ya bawa FRSC damar aiki a titunan da ba na tarayya ba, don haka tsayawa, bincike, da cin zarafi da jami'an na FRSC ke yi a ciki da wajen birnin Kano ya sabawa kundin tsarin mulki.
3. Dokar hana ci gaba da cin zarafi (Perpetual Injunction), Lauyan ya nemi kotu ta hana FRSC da jami’anta ko wakilanta daga ci gaba da tsayawa, tambaya, ko bincike ba tare da doka ba a titunan jihar Kano.
4. Bada hakuri a fili (Public Apology). Ya bukaci kotu ta tilasta FRSC ta bayar da hakuri a babbar jaridar kasa saboda kama shi ba tare da doka ba.
5. Diya na naira miliyan biyar (₦5,000,000) – Ya nemi a biya shi diyyar ci gaba da cin zarafin da ya ce ya sha daga hannun jami’an FRSC.
6. Kudin shari’a (₦1,000,000) – Ya bukaci a biya shi kudin da ya kashe wajen shigar da wannan kara.
7. Duk wani umarni da kotu ta ga dama a karkashin halin da ake ciki.
A cewar lauya Abba Hikima, hukumar FRSC na ci gaba da tsayawa da bincike a cikin garin Kano duk da cewa dokokin kasa sun hana su aiki a titunan da ba na gwamnatin tarayya ba. Ya ce hakan yana tauye ‘yancin mutum da kundin tsarin mulki ya bayar.
An shigar da karar a ranar 8 ga watan Yuli, 2025, kuma za a gudanar da sauraron karar a wani lokaci da kotu za ta sanar nan gaba.