Rikicin masarautu: Ana zargin tawagar Aminu Ado ta kai hari gidan Sarkin Kano Sanusi
Haryanzu rikicin cikin gida na bangaren masarautar Kano na kara ruruwa, a jiya da misalin karfe 01:00 na rana aka hangi tawagar tsohon sarki Alh. Aminu Ado Bayero ta zo wuce wa ta kofar Gidan sarki Khalifa Sanusi Lamido Sanusi.
Sakamakon ya dawo daga wata tafiya, inda ya zarce zuwa Gidan mariyagi Alhaji Aminu Dantata domin gabatar da Ta'aziya.
Sai dai kuma bayan karasowa tawagar ta sa Kofar Kudu, aka hangi wasu matasa daga cikin tawagar tasa sun farma jama'a dake cikin filin Kofar Kudu,
Wanda suka runga amfani da duwatsu suna jifan jama'a, sannan suka yi amfani da makamai wajen yaga hoton Sarki Sanusi dake kofar kudu, dama ragowar dake kan titin zuwa Gidan Sarkin.
Wata majiya ta rawaito cewar cikin wannan rikici ya yi silar mutuwar mutum guda.
Wannan hari shine hari na 3 da tawagar tsohon sarki Alh Aminu Ado Bayero suna kaiwa a cewar bangaren Sarki Sanusi.
Rikicin masarautun dai ya samu asali tun cire rawani da Tsohon Gwamna Ganduje ya yi wa Sarki Sanusi wanda ya nada Aminu Ado a matsayin Sarki, wanda shima Gwamna mai ci Abba Gida-Gida ya yi amfani da damar sa wajen cire Aminu Ado, inda ya dawo da Sanusi II.
Har zuwa wannan lokaci rikicin masarautun na gaban kotu.