SUBEB ta saki sakamakon jarabawar Malamai na BESDA a Kano
Hukumar Ilimin Bai É—aya ta Jihar Kano (SUBEB) ta sanar da sakin sakamakon jarabawar da malaman BESDA suka rubuta a baya-bayan nan.
Wannan na cikin sanarwar da maʼaikatar ilimi ta jihar Kano ta fitar a Jumuʼar nan.
Ta ce an bude shafin duba sakamakon daga Juma’a, 11 ga Yuli zuwa Lahadi, 13 ga Yuli, 2025 kawai.
Sanarwar ta ce domin duba sakamakon, malami zai shiga shafin intanet na www.kanosubeb.org.ng.
Za a yi amfani da sunan Karamar Hukuma a matsayin User ID (kamar: DALA, RIMIN GADO, da sauransu), sannan a saka lambar BESDA ko na jarabawa a matsayin Password.
Hukumar ta bayyana cewa dole ne a rubuta dukkan bayanan cikin babban baki (CAPITAL LETTERS).
An bukaci malamai su tabbatar sun duba sakamakonsu kafin a rufe damar shiga shafin a ranar Lahadi.