Da Dumi-Dumi APC a Kano ta buƙaci hukumar INEC ta soke zaben cike gurbi na Shanono/Bagwai da Ghari dake gudana a halin yanzu
Jam’iyyar APC ta roƙi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) da ta soke zaɓen cike gurbi na mazabar Shanono/Bagwai da kuma karasa zaɓen Ghari da aka gudanar a jihar Kano.
Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Felix Morka, ya fitar ranar Asabar a Abuja.
APC ta ce zaɓen bai dace da ka’idojin gaskiya da adalci ba saboda tashin hankali da kuma rikicin da ya mamaye wuraren kada kuri’a.
Jam’iyyar ta bayyana cewa rahotanni daga Shanono, Bagwai da Ghari sun nuna cewa jama’a sun tsere daga rumfunan zaɓe, yayin da jami’an tsaro suka kasa shawo kan ‘yan daba da ke tayar da hankali.
Sanarwar ta ƙara da cewa ci gaba da gudanar da wannan zaɓe a irin wannan yanayi zai zama tamkar yi wa dimokuraɗiyya fyade tare da fito da sabuwar mummunar hanya ta tafka maguɗi.