Zaɓen cike gurbi a Kano: An kama ƴandaba sama da 100 da ake zargi da yunkurin tada tarzoma - INEC
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa an kama fiye da mutane da ake zargin ƴandaba ne sama da ɗari, yayin da jami’an tsaro su ka yi nasarar dakile yunkurinsu na tada hargitsi a zaɓen cike gurbi na majalisar jiha a mazabar Bagwai/Shanono da ke jihar Kano.
Kwamishinan Zaɓe na INEC a Kano, Ambasada Zango A. Abdu, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da ƴan jarida kan yadda ake gudanar da zaɓen a karamar hukumar Bagwai a yau Asabar.
A cewarsa, rundunar ƴansanda ta tabbatar masa cewa an kama fiye da ƴandaba 100 kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.
“An kama fiye da ɗari. Ƴansanda sun tabbatar mana. Ku ma kun gani da idonku. Tsarin yana ci gaba kuma za a gurfanar da su,” in ji shi.
Abdu ya ƙara da cewa an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali domin babu wani rahoton tashin hankali da aka samu har zuwa yanzu, yana mai yabawa da yadda aka samar da tsaro a wuraren.
“Ina matuƙar jin daɗi, musamman yadda aka tsara tsaro, an tura jami’an tsaro da dama tare da sintiri. An dakile dukkan ’yan daban, an kwantar da su. Tsarin yana tafiya lafiya lau, lallai na yi matuƙar gamsuwa,” in ji shi.
Kwamishinan ya bayyana cewa yawancin wuraren zaɓe sun fara gudanar da aikin tun da karfe 8:30 na safe.
Sai dai ya ce an samu ɗan jinkiri a wurare kaɗan sakamakon lalacewar wasu motocin da ke ɗauke da kayan zaɓe da jami’ai.