Dadumi-Dumi Gwamnatin Kano ta bude Portal na rarraba irin Bishiyu, masu nema su yi Maza su cike
Daga Maryam Gadon Kaya
Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano na sanar da al’umma cewa a fara tantancewa da kuma rabon irin bishiyoyin da ake bayarwa a karkashin shirin gwamnatin jihar na Dasa Bishiyoyi Miliyan Biyar a jihar.
A halin yanzu, sama da ƙungiyoyi 200 ne suka riga suka nemi irin bishiyoyin, kuma ana ci gaba da tantancewa tare da rarraba musu irin kamar yadda ya dace.
Ma’aikatar na kuma gayyatar sauran kungiyoyi, cibiyoyi, da al’umma baki É—aya da ke sha’awar samun irin bishiyoyin da su yi rajista ta hanyar wannan adireshin:
👉 https://environment.kn.gov.ng/programs/five-million-trees