Daga Hafsat Muhammad Abuja
Ƙwararrun likitocin mata sun yi gargadi cewa yawan amfani da maganin hana ɗaukar ciki na gaggawa na iya jawo tangardar al’ada da sauran matsalolin lafiyar haihuwa.
Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Likitocin Haihuwa da Cutukan Mata ta Najeriya (SOGON), Farfesa Chris Aimakhu, ya bayyana cewa mata da dama sun fara amfani da maganin kamar magani na kullum, duk da cewa an tsara shi ne kawai don lokutan gaggawa kamar jima’i ba tare da kariya ba, fashewar kwaroron roba ko fyade.
Aimakhu ya ce amfani fiye da kima kan jawo jinkiri ko rashin daidaiton haila, gazawar maganin wajen hana ciki da kuma haɗarin kamuwa da cututtukan jima’i, domin ba ya kare mace daga irin waɗannan cututtuka.
Shi ma wani likitan mata, Dakta James Odofin, ya ce wasu mata na amfani da Postinor akai-akai, abin da ya kira amfani fiye da kima, yana mai bayyana cewa wannan magani bai dace da amfani na kullum ko na dogon lokaci ba.
Likitocin sun shawarci mata su yi amfani da hanyoyin kariya mafi inganci kamar kwaroron roba, allurar rigakafi ko na’urar IUD, tare da gujewa dogaro da maganin na gaggawa.