Gwamnatin Kano ta kama wasu mutane bisa sare wasu bishiyoyi da suka shafe gwamman shekaru ba da izini ba
Ma'aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane bisa fara sare wasu bishiyoyi a unguwar Na'ibawa, layin ÆŠan Hassan a jihar.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir Muhammad Hashim, a wata sanarwa da ya aikewa Jaridar Neptune Prime, ya ce bishiyoyin sun kwashe gwamman shekaru su na bada kariya Da inganta muhalli ga al'ummar yankin.
Ya ce nan take, aka dakatar da saran bishiyun tare da kama dukkan masu laifin, da kuma kwace kayan aikin hannunsu, ciki har da inji na sare bishiya (chainsaw).
A cewar Kwamishinan, an mika waÉ—anda aka kama din ga jami’an tsaro domin daukar matakin da ya dace bisa doka.
Kwamishinan ya kara jaddada cewa sare bishiya ba tare da izinin gwamnati ba babban laifi ne, wanda ka iya jefa mutum cikin gidan yari – ko da bishiyar a cikin gidansa take.
Ya kuma yi gargadi ga duk masu amfani da inji na sare bishiya (chainsaw) ko sauran kayan yankan bishiya ba bisa ka’ida ba, da su sani cewa gwamnati ta haramta hakan, kuma ba za a lamunta da shi ba.