Hamshaƙin attajiri Aliko Dangote ya ci gaba da riƙe kambinsa na mutum mafi arziƙi a Afirka, inda ya mallaki kimanin dalar Amurka biliyan $24.4 a yanzu.
Hamshakin Attajiri Dan asalin Jihar Kano Alh. Aliko Dangote a yanzu shi ne mutum na 88 a masu kuɗin duniya a sabuwar ƙididdigar da Mujallar Forbes ta gudanar a bana.
Dangote ya ninninka takwarorinsa ‘yan Najeriya a yanzu da tazara mai yawa a inda Abdulsamad Rabiu shima da ya fito daga Jihar Kano ke biyo da shi da dala biliyan $7.2 da matsayi na 516 a duniya, sai Mike Adenuga da dala biliyan $6.3 da matsayi na 592 a duniya, sai kuma Femi Otedola da dala biliyan $1.5 matsayi na 2424 a duniya.
Tun a shekarar 2008 ne Dangote ya fara shiga jerin sunayen masu kuɗin duniya na Forbes kuma ya ci gaba da riƙe muƙamin tun daga shekarar 2011, wanda kuma ya riƙe matsayin mutum mafi arziki a Afirka na tsawon shekaru 14 a jere.