Kungiyar Tsofaffin ƴan Majalisa na Kudu ta bayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da zasu goyawa baya a zaben 2027.
Sanarwar da aka fitar bayan taron kolin da aka gudanar a Abeokuta ta ce goyon bayan ya samo asali ne daga bukatar tabbatar da adalci, haɗin kan ƙasa da ci gaban Najeriya.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba na musamman wanda ya cancanci goyon bayan ’yan Najeriya baki ɗaya don ya ci gaba bayan 2027.
Haka kuma, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ken Nnamani, da Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, sun yaba da jagorancin Tinubu tare da kira ga ƙara haɗin kai domin ci gaban ƙasa.
Taron ya samu halartar manyan tsofaffin ’yan majalisa da shugabannin siyasa daga sassan ƙasar.