Daga Hafsat Muhammad Abuja
Cibiyar Aikin Jarida ta Ƙasa-da-Ƙasa, wato International Press Institute (IPI), wacce ke fafutukar kare ’yancin kafafen yada labarai da kuma tabbatar da walwalar samun bayanai, ta nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar matsin lamba da takura wa ’yan jarida a Æ™asar nan.
Shugaban IPI Nigeria, Musililu Mojeed, ya yi wannan gargadi ne a wani taron liyafa da ƙungiyar ta shirya a ranar Asabar a Abuja, domin girmama daya daga cikin membobinta, Hajiya Hadiza Hussaina Sani, tsohuwar Daraktar Sashen fasahar zamani ta gidan rediyon ƙasa na VON, wacce ta kammala aikin gwamnati bayan cika shekara 60.
A jawabin sa a wajen taron, Mojeed wanda shi ne Babban Editan Premium Times, ya bayyana damuwarsa kan matakai na baya-bayan nan da suka hada da hana shirin siyasa a kai tsaye a Kano, tare da kama ’yan jarida a jihohin Ekiti da Neja.
Ya ce: “A jihar Akwa Ibom, gwamnatin jihar ta kori tawagar Channels TV daga Cibiyar ’Yan Jarida da ke fadar gwamnatin Uyo, bayan sun wallafa bidiyon da gwamnan ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
“Haka kuma a jihar Kebbi, wani É—an jarida mai suna Hassan Mai-Waya Kangiwa an tsare shi bayan ya fallasa sakaci a wani asibiti. A gefe guda kuma, tsohon ma’aikacin ThisDay, Azuka Ogujiuba, an cafke shi tare da cin zarafi saboda aikin jarida kawai.
“Kullum idan ka tashi, sai ka ji an sake tsananta wa kafafen yada labarai,” in ji shi.
Mojeed ya bukaci da ci gaba da fafutuka da gwagwarmaya domin kare Æ´ancin kafafen yada labarai da kuma bunÆ™asa aikin jarida mai cin gashin kansa. Ya ce kare ’yancin ’yan jarida da goyon bayan aikin jarida mai zaman kansa muhimmin abu ne a tsarin kafafen labarai na Najeriya.