A yau Litinin ne Matatar Dangote za ta fitar da motoci sama da 1,000 masu amfani da iskar gas dauke da man petur, a matakin farko na shirin rarraba man kai tsaye zuwa jihohi.
A bangarenta kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta ce ta shirya tsaf domin karɓar motocin man a tashoshinta daban-daban da ke a fadin Najeriya.
masu ruwa da tsaki a matatar man ta Dangote sun shaidawa manema labarai cewa za'a fara rarraba man kai tsaye a matsayin wani ɓangare na bikin cika shekara guda cif da fara samar da fetur daga matatar.