Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kano (KEDCO) ya tuhumi Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) bisa zargin mutuwar wasu majinyata masu bukatar agajin gaggawa sakamakon katsewar wutar lantarki.
A ranar Lahadin da ta gabata ne AKTH ya nuna matukar damuwarta kan lamarin, inda ta ce da a ce an ci gaba da samun wutar lantarki za a iya dakile asarar rayuka.
Amma da yake mayar da martani, shugaban sashen sadarwa na KEDCO, Sani Bala Sani, ya ce asibitin na kokarin bata masu ne saboda an maido da hasken lantarki tun kafin faruwar matsalar.
Sani ya ce lamarin rashin lantarkin ya samo asali ne daga wani tsari da ake yi na raba layin lantarkin harabar asibitin da ginin cibiyoyin lafiya da rukunin gidajen kwanan ma’aikatan.