Allah ya yiwa tsohon sakataren gwamnatin Kano, Alhaji Sadauki Kura, rasuwa da safiyar yau Lahadi a asibitin Airforce da ke Kano.
Alhaji Sadauki Kura wanda ya rasu yana da shekaru 85 a duniya, ya taɓa zama manajan bankin Union Bank inda daga nan ne aka aro shi ya zo yayi sakataren gwamnatin Kano a lokacin gwamna Hamza Abdullahi.
Ya rasu ya bar matansa biyu da yaya da jikoki da dama.
Tuni aka yi jana’izar sa a gidansa da ke Gandu kusa da kwalejin Rumfa da karfe 11 na safe.
Allah ya yi masa gafara ya sa Aljannah Firdausi ce makoma.