Kungiyar lauyoyin Kano sun buƙaci a sake bude shari'ar zargin kisan kai da ake wa Dan majalisa Tarayya Alhassan Ado Doguwa
Kungiyar lauyoyin ƴan asalin jihar Kano ta bukaci a sake bude shari’ar zargin kisan kai da ake yi wa dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Doguwa da Tudun Wada, Hon. Alhassan Ado Doguwa, dangane da abin da ya faru a lokacin zaben 2023.
A cikin wata takardar koke da kungiyar ta aikewa Kwamishinan Shari’a na jihar Kano, mai kwanan watan 11 ga Satumba, lauyoyin sun bukaci a sake farfado da bincike kan rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa.
Kungiyar ta bayyana cewa duk da girman zargin da ake yi, an dakatar da shari’ar ne bisa dalilai na siyasa, wanda a cewarsu ya saba wa sashe na 33(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya da ke kare hakkin rayuwa na kowanne dan kasa.
Zargin kashe mutane ba karamin lamari ba ne. Ya kamata a bari doka da shari’a su yi aikinsu ba tare da katsalandan ba. Hakan ne kadai zai tabbatar da adalci da kare darajar doka,” in ji kungiyar.
A gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu idan bincike ya tabbatar da laifinsu, ba tare da la’akari da mukami ko matsayin siyasa ba.
Lauyoyin sunce yin watsi da irin wannan shari’a saboda siyasa ba wai kawai yana tauye hakkin wadanda suka rasa ‘yan uwansu ba ne, hakan kuma yana raunana tsarin dimokuradiyya da amincewar jama’a da dokokin kasa.
A karshe, kungiyar ta roki gwamnatin Kano da sauran hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da cewa an bi doka yadda ya kamata domin iyalan mamatan su samu adalci.