Sabon Shugaban Jami’ar Bayero (BUK), Farfesa Haruna Musa, ya bayyana cewa jami’ar ta fara shirin gina gidaje 500 ga ma’aikatanta domin magance matsalar karancin gidaje da ta daɗe tana damun al’ummar jami’ar.
Farfesa Musa ya bayyana haka ne yayin taron Registry Roundtable karo na biyu da aka gudanar a dakin Majalisar Jami’ar a makon da ya gabata.
Ya ce tun bayan hawansa shugabancin jami’ar kasa da wata guda, an fara aiwatar da shirin da ya kunshi manyan tsare-tsaren jin dadin ma’aikata.
Ya ce tuni shugabancin jami’ar ya shiga tattaunawa da Bankin Lamunin Gida na Ƙasa (FMBN), kuma an kai matakin ci gaba wajen tabbatar da aikin.
Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a sanya hannu kan yarjejeniya domin aiwatar da aikin gina gidajen.
Shirin gina gidaje 500 na daga cikin muhimman ayyuka da ake ganin zai inganta jin dadin ma’aikata tare da kawo sauƙi ga matsalar gidaje da ke addabar jami’ar tsawon shekaru.