Daga Hafsat Muhammad Abuja
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta koka kan yadda ake ƙara yawaitar kama ƴan gwagwarmaya da ke sukar muradan gwamnatoci a ƙasar nan.
Kungiyar ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta nuna damuwa kan yadda ake amfani da wasu tsare-tsare wajen tsoratarwa da take ’yancin faɗar albarkacin baki.
Sanarwar ta ce daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su a baya-bayan nan akwai Hassan Kangiwa daga Jihar Kebbi, Hussaini Bello Nakura daga Jihar Adamawa da kuma Daure David daga Jihar Bauchi.
Ƙungiyar ta ce gwamnati na nuna rashin juriya ga waɗanda ke bayyana ra’ayoyinsu ta kafafen sada zumunta ko kuma a bainar jama’a, abin da ta kira take haƙƙin bil’adama.
Ta kuma bayyana cewa kama mutum saboda sukar gwamnati ko jami’anta ba shi da tushe balle makama.
Amnesty International ta yi kira ga hukumomi su daina kama ’yan ƙasa saboda sukar shugabanni,
Maimakon hakan su mayar da hankali wajen magance matsalolin da suka shafi cin hanci, nuna son kai da halin ƙuncin tattalin arziƙi, waɗanda ke tilasta jamaʼa su koka.