Ƴan sanda sun kama bakaniken da ya tsere da motar kwastomarsa a Jihar Kano
Rundunar ƴan sanda ta Jihar Kano ta kama wani bakanike mai shekaru 42, Abubakar Yakubu, bisa zargin guduwa da motar abokiyar huldarsa bayan ta ba shi mota don gyara.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a Kano.
A cewar sa, wanda ake zargin, mazaunin unguwar Sharada ne, kuma ya karɓi motar daga wata mata a ranar 28 ga Agusta, 2025, da sunan zai gyara mata AC, amma daga bisani ya tsere da motar.
Ya bayyana cewa Kwamishinan Ƴan sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya hanzarta tura tawagar jami’an sirri, kamar yadda Sufeton ƴan sanda na ƙasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya bada umarnin a rika yi domin ƙarfafa aikin binciken asiri da sintiri a fadin ƙasar.
A cewar Kiyawa, An bi sawun wanda ake zargi har zuwa jihar Kaduna, inda aka gano ya sayar da motar kirar Mercedes-Benz ta hanyar yin kakara aka bashi Toyota Corolla bayan ya cika Naira miliyan 7.”
An kama shi tare da kwato Toyota Corolla ɗin, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano motar Mercedes-Benz ɗin da ya sace.