Gwamnatin Kano ta rufe wasu makarantun masu zaman kansu
Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu da na sa kai ta Jihar Kano (KSPVIB) ta dauki matakin rufe wasu makarantu guda takwas da ke aiki a fadin jihar, bisa dalilai na karya dokoki da kuma sabawa Æ™a’idojin gudanarwar hukumar.
A yayinda yake ganawa da manema labarai, Shugaban hukumar Kwamared Baba Umar ya ce rufe makarantun ya zama wajibi saboda karya dokokin kara kuÉ—in makaranta da rashin yin takardun na izinin gudanarwa.
Wadannan makarantu sun hada da:
1. Prime College Kano – Alu Avenue, Kano
2. Darul Ulum – Hotoro (Ahmad Musa Road)
3. Gwani Dan Zarga College – (Kofar Waika)
4. Awwal Academy – Rimi (Sumaila)
5. Dano Memorial College – (Sumaila)
6. Unity Academy – Wudil
7. Nurul Islam School
8. As-Saif College.
A makon da ya gabata ne shugaban hukumar Baba Umar ya bada wa’adin mako biyu a kai korafin duk wata makaranta mai zaman kanta da ta kara kuÉ—in makaranta,Inda yace mutane sun bada hadin mai kuma su sun dauki matakin da ya dace na rufe irin wadannan makarantu tare da gurfanar da su gaban kotu.
Shugaban yace a bisa umarnin Kotu,an dakatar da ayyuka a wadannan makarantun har sai abinda alkali ya yanke hukunci akai.
Yace wasu sun ƙara kuɗin makaranta ba tare da amincewar gwamnati ba.
Baba Umar ya kuma ce sun gano matsalar tsaro da rashin isasshen tsari a cikin gine-ginen wasu daga cikin makarantun.
Sai kuma rashin ingantattun kayan aiki da guraben koyarwa da ya dace da Æ™a’idar karatun zamani.
Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki ya zama dole ne domin tabbatar da cewa yara na samun ilimi mai inganci, tare da kare iyaye daga karÉ“ar nauyin kuÉ—aÉ—en da aka É—ora musu ba bisa Æ™a’ida ba.
Ta kuma yi gargadi ga sauran makarantu masu zaman kansu a jihar da su kiyaye doka da Æ™a’idojin gwamnati, inda ta ce duk wanda ya ci gaba da karya dokoki, ba za a yi masa rangwame ba.
Daga karshe ya nemi jama’a su cigaba da kai Rahoton duk makarantar da ta saba doka yana mai cewa ba’a kafa hukumar sa domin kuntatawa makarantun masu zaman kansu ba saidai domin dawo da su kan hanya idan sun kauce.