Jami’ar European-American University ta karyata rahotannin da ke cewa ta gudanar da taron karramawa a NICON Luxury Hotel, Abuja. Ta bayyana cewa wannan taro bada masaniyar ta shirya ba.
Jami’ar ta nesanta kanta daga karramawar da aka ce an bai wa Dauda Kahutu Rarara da wasu, tare da jaddada cewa Musari Audu Isyaku da Idris Aliyu ba su da hurumin wakiltar jami’ar, inda aka kuma soke matsayin Aliyu saboda rawar da ya taka a wannan zamba.
Ta kara da cewa tsohuwar shugabar jami’ar, Dr. Mrs. Josephine Egbuta, ba ta da hurumin wakiltar jami’ar, yayin da shugaban yanzu shi ne Professor Luca Scotto di Tella.
Jami’ar ta sha alwashin tuntubar hukumomin Najeriya domin dakatar da masu sayar da takardun bogi da sunanta.
Jami’ar ya bayyana haka ne a shafinta na yanar gizo.