Rahota ya bayyana cewa talauci da matsin tattalin arziki na tura daruruwan ƴan Nijeriya zuwa siyar da ƙodarsu,
Inda aka gano sama da Æ™oda 651 aka sayar ba bisa Æ™a’ida ba tsakanin shekarar 2015 zuwa 2020, tare da samun kimanin dala biliyan 41 a kasuwar fataucin gaÉ“oÉ“i ta É“oye.
Farfesa Aliyu Abdu babban likitan nephrologist a Jami’ar Bayero Kano (BUK), ya bayyana hakan a wani taron Æ™ara wa juna sani da aka gudanar a Abuja, yana mai kiran wannan kasuwanci Æ™azamar sana’ar Duniya da ke haÉ—a dillalai, likitoci, Æ´an damfara da talakawan da ke neman kuÉ—in fita daga talauci.
Ya ce masu safarar sassan jiki suna haɗa masu son siyar da ƙoda da masu kuɗi, suna amfani da talauci a matsayin hanyar tara riba.
Duk da cewa Dokar Kiwon Lafiyar Nijeriya ta 2014 ta haramta sayar da gaɓoɓi tare da hukunta masu laifi, raunin aiwatar da doka ya bai wa kasuwar bayan fage damar bunƙasa.
Rahotanni sun nuna cewa a duk shekara ana sayar da ƙoda sama da 10,000 a Duniya ba tare da kulawa da lafiyar masu siyar da su ba, abin da ke barin su cikin raunin lafiya, matsin kuɗi da damuwa.