Kotu a Kano ta tura matashin da ake zargi da kashe Mahaifinsa gidan Yari
Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 7 Æ™arÆ™ashin jagorancin Mai Shari’a Aminu Adamu ta tura wani matashi mai suna Aminu Ismail, É—an asalin garin Ganbai a Karamar Hukumar Ajingi, zuwa gidan yari bisa zargin kashe mahaifinsa, Dahiru Ahmad.
Lauyan Gwamnati mai gabatar da ƙara, Barista Lamido Abba Sorondinki, ne ya roƙi kotu ta karanta wa wanda ake tuhuma tuhumar da ake masa, sai dai Aminun ya musanta.
Kotun ta bayar da umarnin a mayar da wanda ake tuhuma gidan yari tare da É—age sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Nuwamba 2025 domin fara sauraron shaidu.
Ana zargin matashin da kashe mahaifinsa saboda ya hana shi yin ƙarin aure, a watan Afrilu 2024.