Majalisar Dattawa ta amince da nadin sabbin Hafsoshin Tsaron Najeriya
Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da naÉ—in sababbin hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar a ranar Juma’ar da ta gabata. Wannan mataki na zuwa ne bayan tantancewa da tattaunawa mai zurfi da majalisar ta gudanar da su yau Laraba.
Wadanda aka amince da su sun haɗa da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar Waidi Shaibu a matsayin Hafsan Sojan Ƙasa, Rear Admiral Idi Abbas a matsayin Hafsan Sojan Ruwa, da Air Marshall Kennedy Aneke a matsayin Hafsan Sojan Sama.
A yayin zaman tantancewar, sabbin shugabannin rundunonin sun gabatar da tarihin ayyukansu da gogewarsu a harkar tsaro, tare da amsa tambayoyi daga ‘yan majalisar kan hanyoyin da za su inganta tsaro da tabbatar da zaman lafiya a Æ™asar.