Kungiyar Izala takasa ta buƙaci a sasanta dambarwar Sheikh Triumph cikin lumana
Shugaban Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta tarayyar Nigeria, Ash-Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau , ya yi kira da a kwantar da hankali da nuna haƙuri wajen tafiyar da rikicin addini da ke ci gaba a Kano, inda ya gargadi mutane da su guji amfani da lamarin don haifar da rarrabuwar kawuna a cikin al’ummar Musulmi.
A lokacin da yake gabatar da wa’azi a makon jiya wajen taron ƙungiyar ‘Federation of Ahlusunnah Organization in Nigeria’ (FAFSON) da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, Sheikh Bala Lau ya yaba da hangen nesa da kwarewar Darakta Janar na Hukumar Tsaro na Farin kaya (DSS), Mista Tosin Ajayi, wajen tabbatar da lamarin zuwa hanyar zaman lafiya ba tare da zuwa kotu ba.
“Ina yabawa shugabancin DSS bisa tabbatar da cewa an tafiyar da wannan al’amari cikin hikima da lumana.
Kai shi kotu zai iya tada jijiyoyin wuya kuma ya tsawaita rikicin.
Abin da al’ummar Musulmi ke buƙata a yanzu shi ne hikima, haƙuri da haɗin kai,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta ci gaba da zama tsaka-tsaki, yana jaddada cewa shiga gefen kowane ɓangare na iya ƙara rarrabuwar kai da lalata zaman lafiya a jihar.
“A irin wannan lokaci, bai kamata gwamnati ta nuna tana goyon bayan ɓangare guda ba.
Adalci da gaskiya suna buƙatar a tsaya a tsaka-tsaki.
Aikinmu a matsayin shugabanni shi ne kiyaye zaman lafiya, ba ƙara wa rikici wuta ba,” in ji Sheikh Bala Lau.
Jawabansa sun biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da aka gabatar tare da mayar da martani ga Majalisar Shura ta Jihar Kano kan zargin kalaman batanci da ake alakanta Shi da Sheikh Lawan Shuaibu Abubakar Triumph.
Majalisar ta bayyana cewa za ta saurari masu ƙorafi da kuma malamin kafin ta ba da wani shawari ga gwamnati.
Sai dai Sheikh Bala Lau ya yi kira ga Musulmi da kada su bari zarge-zargen su rinjaye su, yana gargadi cewa irin waɗannan muhawarori idan ba a kula ba za su iya bata sunaye kuma su kau da hankali daga babbar manufar ƙarfafa addini.
“Kano ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Arewa maso Yamma. Bai kamata mu bari rikice-rikicen su lalata wannan tarihi ba.
Mu kiyaye harsunanmu, mu guji zagin juna, mu kuma yi aiki tare domin bunƙasar Musulunci da al’ummarmu,” in ji shi.