Shugabancin kungiyar Allah ya maimaita Abba 2027 movement na Jihar Kano ya tabbatar da Hon Jameel Lawan Yakasai P.A a matsayin Coordinator na karamar hukumar Birnin Kano "Kano Municipal".
Wannan na zuwa ne a ya yin babban taron da Kungiyar ta gudanar a yau Asabar 26-09-2026, taron wanda akayi shi a ofishin Jam'iyyar APC dake Hotoro Karamar Hukumar Nassarawa.
Jameel P.A dan gwagwarmaya ne a fannin siyasa, wanda ya zama tsohon ma'aikacin Nasara Radio, kuma babban mataimaki na musamman ga Shugabar Talabijin na ARTV, ya yi Kungiyoyin siyasa da dama a fanoni daban daban.