Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya ruwaito cewa wacce ake zargin na zaune ne a lamba 5, titin Amadiya, unguwar Olomore a Abeokuta.
NAN ya kuma ruwaito cewa waccw ake karar na fuskantar tuhume-tuhume guda uku na cin zarafi, tada zaune-tsaye da kuma yin abin da zai jefa rayuwar mai korafin cikin hadari.
Mai gabatar da kara, Sifeto Olaide Rawlings, ya shaidawa kotun cewa wacce ake tuhuma ta aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Afrilu da misalin karfe 1:00 na rana a unguwar Olomore dake Abeokuta.
Ms Rawlings ta ce wacce ake tuhumar ta ci zarafin wani Silas Olaleye ta hanyar turo shi daga kan tsani yayin da ya ke gudanar da aikinsa na halal, wanda hakan ya jawo masa karaya a kafarsa ta dama.
A cewarta, laifukan sun saɓa wa sashe na 338, 343, 355 da 249 na kundin laifuffuka na jihar Ogun, 2006.
Sai dai wacce ake tuhumar musanta laifin da ake tuhumar ta da shi.
Alkalin kotun, M.O. Osinbajo, ta bayar da belin wacce ake kara a kan kudi N100,000, tare da mutum daya da zai tsaya mata.
Bayan haka, ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 28 ga Afrilu domin ci gaba da shari’ar.