INEC ta bayyana Alh. Aminu Sa'adu na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar jiha ta ungogo in ya samu kuri'u
31,135. shi kuma Umar badaru ya samu 24,430
Waɗannan sune tarin alƙawuran daya ɗauka zai yi idan ya samu dama.
1_ Biyan kudin maganin marasa lafiya wadanda basu da karfin siya
2__ Tallafawa mutane masu san su kara jari a sana'o'in su maza da mata
3__ Tallafawa mutane ta fuskar neman ilimi
4_ Daukar nauyin yiwa marasa laifi aiki
5__ Tallafawa mutane musamman wadanda zasu aurar da yayansu, wasu ana siya musu katifa, wasu kayan dakin baki daya ake siya musu. Idan namiji ne mafi karancin abinda Hom Aminu Sa'adu ke bayarwa shine #30,000 domin biyan sadaki.
6__ Bada tallafi domin gudanar da ayyuka mazabu 11 dake fadain karamar hukumar Ungogo. Wannan ya hada da gyaran hanyoyi, gadoji, gyaran burtsatse, siyan transformer, gina makarantu, siyan filin makabarta da sauran su.