Alkalin kotun, Abdullahi Abdulkareem, ya raba auren ne kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada, bayan da Yahaya ya nemai sakin bisa dalilin cin amana.
Abdulkareem ya umurci Adejoh da ta yi “Iddah” ta wata uku kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kafin ta sake yin wani auren.
Ya kara da cewa batun kula da yara da mai shigar da kara ya gabatar a gaban kotu ya kamata a shigar da shi a matsayin wata kara ta daban.
Tun da fari dai wanda ya shigar da karar, ya shaidawa kotun cewa ya auri wacce ake kara bisa shari’ar Musulunci a ranar 14 ga Satumba, 2009 kuma sun haifi ‘ya’ya biyu masu shekaru 14 da 12.
Ya ce ya lura cewa wacce ya ke kara ta fara mu’amala da maza.
“Na ga Adejoh ta na buya a cikin kicin ta na waya da wani mutum, kuma da na tuhume ta, doke ni ta zage ni” in ji Yahaya.
Ya ce ya yi rashin lafiya a cikin watanni hudu da suka gabata, an kwantar da shi a asibiti, daga bisani aka kai shi kauyensu da ke Kogi amma matar ta sa ba ta taba zuwd ta duba shi ba, kawai ta ci gaba da harkokin ta.
“Babu soyayya da zaman lafiya a auren, ina son a raba auren,” in ji shi.