Haƙiƙa mun sani, kuma mun yarda, cewa ba Nijeriya ba ce za ta yaƙi ƙasar Nijar, ƙungiyar ECOWAS ce.
Kamar yadda Malam Hasheen ya yi bayani, ƙungiyar ECOWAS ƙungiya ce ta haɗakar ƙasashen yammancin African, irin su: Benin da Burkina Faso da Cabo Verde da Cote d'Ivoire da Gambia da Ghana da Guinea da Guinea-Bissau da Liberia da Mali da Niger da Nigeria, Senegal da Sierra Leone da kuma Togo. Waɗannan ƙasashen sun haɗu ne a ƙaƙashin ƙungiyar bisa yarjejeniyar aiki tare da kuma taimakon kai-da-kai don tabbatar da wanzuwar demokradiyya a tsakaninsu. Dalilin da ya sa wasu suke ganin kamar Nijeriya ce za ta yaƙi Nijar shi ne, saboda kasancewarta uwa ko kuma kan gaba a cikin ƙungiyar ECOWAS. Wannan kuma ya biyo bayan ƙarfin tattalin arzikin da take da shi da kuma ƙarfin soja da yawan al'umma. Duk da yake masana da kuma ƙwararru suna ganin ƙasar Nijeriya ita kaɗai (ba tare da haɗaka da wata ƙasa ba) za ta iya yin karin kumallo da sojojin juyin mulkin Nijar ta mayar da farar hula kan mulki, amma kuma wasu na ganin reshe zai iya juyewa da Mujiya, saboda yaƙi ɗan zamba ne. Ko ba don wannan ba ma, akwai wasu dalilai da ya sa kaso mai yawa na al'ummar Nijeriya (ko kuma Arewancin ƙasar) ba sa goyon bayan yunƙurin ECOWAS. Daga cikin akwai:
1- Arewancin Nijeriya zai shiga tsaka-mai-wuya/hatsari saboda yadda abin zai shafi yankin ta dalilin makwabtakar da yake yi da ƙasar Nijar (musamman a wannan lokacin da yankin yake farfaɗowa daga cikin yaƙin da aka shafe sama da shekaru goma ana yi da Boko haram). Wannan ya sa mafi yawa ko nace masu hangen nesa ba sa goyon baya.
2- Dalili na biyu shi ne, lamarin zai shafi fararen hular da suke ƙasar Nijar da kuma waɗanda suke Arewancin Nijeriya. Domin yaƙin ba a iya kan sojoji zai tsaya ba (mu dubi ƙasar Sudan a matsayin misali).
3- Sannan kuma zai ƙara durƙusar da kasuwancin da ke tsakanin Nijar da Nijeriya ko kuma Arewancin Nijeriya.
4- Rashin sanin abin da yaƙin zai iya haifarwa, saboda yaƙi ɗan zamba ne. Shin ECOWAS ce za ta yi nasara? Ko kuwa sojojin juyin mulkin Nijar ne? Sannan kuma menene makomar al'ummar Nijar dana Nijeriya bayan yaƙin?
5- Mu ('yan Nijeriya) da muke ƙarƙashin demokradiyya a yanzu, me ta tsinana mana a tsawon lokacin da aka kwashe ana yi har da za mu jefa rayukan wasunmu a hatsari? (wannan tunanin ire-irena ne masu ƙananan hange).
Waɗannan dalilai da kuma ƙarin wasu su suka sa mafi yawan al'ummar Nijeriya ko kuma na Arewacin Nijeriya ba sa goyon bayan yunƙurin ECOWAS na amfani da ƙarfin soja akan ƙasar Nijar. Idan da wata hanyar da ya kamata a ɓullo (ban da yaƙi) domin dawo da farar hula kan karagar mulki a Nijar to muna murna, amma ba mu yarda da yaƙi ba. Idan kuwa babu, to a kyale al'ummar ƙasar Nijar da mu kanmu mu zauna lafiya. Domin ba ƙasar Nijar ba ce kaɗai sojoji suke mulki a cikin Afirka.
Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya a ƙasarmu da makwabtanmu da Afirka da ma duniya bakiɗaya, Amin.
Ɗalibinku,
Mohammed Bala Garba, Maiduguri.
Marubuci/manazarci.
9 Ogusta, 2023.