Mazuna birnin Jaranwala da ke Gabashin Punjab sun ce wasu gomman gine-gine da ke kusa da coci-cocin su ma sun ƙone.
Ƴan sanda suna tsare da wasu masu zanga-zanga fiye da 100, sun kuma ƙaddamar da bincike a kan rikicin.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar, amma sun bayar da tabbacin cewa ba a kashe kowa ba.
Jami'an tsaron sun kuma shigar wani Kirista mazaunin yankin ƙara, bayan sun zarge shi da cin mutuncin addini, laifin da dokar ƙasar ta yi wa tanadin hukuncin kisa.
Duk da cewa Pakistan ba ta taɓa zartar da hukuncin kisa ga masu aikata laifin wulakanta addini ba, irin wannan laifi yana saurin kawo zanga-zanga da tashin hakankali, har ma da kisan waɗanda ake zargi da laifin.