A ranar 26 ga watan Yuli ne ƙungiyar ta tsunduma yajin aiki, sakamakon rashin biya mata buƙatunta da suka shafi inganta aiki, da ta ce gwamnatin ƙasar ta yi.
A baya ƙungiyar ta shirya fara zanga-zangar ne a ranar tara ga watan Agusta a asibitocin gwamnati da ke sassan ƙasar, amma ta dakatar da shirin nata bayan taron gaggawa na shugabanninta.
Shugaban ƙungiyar, Dr. Emeka Orji, ya shaida wa BBC cewa sun janye aniyar tasu ne bayan tattaunawa da ƴan majalisar dokokin tarayya, waɗanda suka nemi uzurin kwana ɗaya don samar da mafita.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da likitoci a Najeriya ke shiga yajin aiki ba.
A shekarar 2020 likitocin sun shiga yajin aiki a lokacin da ake ganiyar annobar Corona don neman inganta albashi da sauran haƙƙoƙinsu.