Dattijo a masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Abdullahi Shu'aibu (Abdu Kano) wanda aka fi sani da Karkuzu na Bodara, ya nemi al'ummar Duniya da su tallafa masa, bisa halin da yake ciki na rashin muhalli da abinci.
Kafar Zinariya dake Internet, ta wallafa bidiyon dattijon yana neman tallafi, musamman a yanzu da lalurar makanta ta sa me shi.
Yace mafi yawan abokansa da suka yi sana'ar fim sama da shekaru 40 da suka gabata, kusan duk sun rasu.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun wasu jaruman masana'antar na neman tallafi akan abinda ya shafi muhalli, abinci ko lalura ba.