Addinin musulunci bai yarda wani ya yi amfani da harshensa wajen cutar da dan uwansa ba, walau ta hanyar aibata shi ko yi masa kazafi da ko kuma fadin duk wani da zai sa wanda aka fadi maganar akansa zai ji ba dadi”.
Shugaban majalisar Limamam masallatan juma’a na jihar Kano, Shekh Muhammad Nasir Adam kuma limamin masallacin juma’a na Shekh Ahmadu Tijjani dake kofar mata ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya gabatar kan illar da harshe ke da shi.
Ya ce Allah da Annabi sun yi bayanai masu yawa a alqur’ani da hadisi kan illar cutar da wani da harshe ta Kowacce fuska.
Ya kuma ce shari’ar musulunci bata yadda mutum ya fadi maganar da babu ita ba.
“Duk wanda ya fadi wata mummunar magana akan dan uwansa Musulmi kuma wani cikin Musulmi ya ji Dadi, to malamin ya ce Allah zai baiwa wanda ya ji dadin cin zarafin zunubi daidai da wanda ya fadi maganar”. Sheikh Muhammad Nasir
Ya kuma yabawa kafafen yada labarai kan hana yin magana ta siyasa a kafar su kai tsaye ba tare da an tantanceta ba.
Shugaban majalisar Limamam masallatan juma’a na jihar Kano Shekh Muhammad Nasir Adam ya kuma yabawa kokarin da gwamnatin jihar Kano ke yi na ganin an daina siyasar cin zarafin al’umma a jihar.